1. MENENE HACKING
Ayayin da wasu sukaji ance hacking, to abin da suke dauka shine, | Ta'addanci ne kawai, ko satar kudi abanki,ko satar wasu mahimman bayanai, ko kuma dai wata mummunar dabi'a A'a bari kuji me hacking yake nufi
Atakaice hacking wata hanyace da Zaka sami damar mallakar ko kutsawa cikin Na'urar daba mallakin ka ba ta hanyar Karya tsaron ta, kenan kamar kayi amfani da rauni na tsaro,domin ka kai zuwa wani abu killatacce da baka da izinin kaiwa gareshi,wannan shine hacking
2. SUWA AKE KIRADA HACKERS
Wanda zamu iya kira da hackers sune, Wanda zasu iya kutsawa cikin Na'urar, ko wani dakin ajiya na internet ba tare da izinin mai mallakar abun ba, amma Idan kana tunanin cewa hackers yan ta'addane akwai, ko kuma hackers wasu masana ne a bangaren tsaron na'ura akwai, A'a bari kugi yadda rabe raben su yake,
3. RABE-RABEN HACKERS
Akwai rabe-raben hackers daban-daban, amma ga jiga-jigai daga ciga cikinsu
- White hat hackers
- Black hat hackers
- Gray hat hackers
** white hat hackers| su white hat sune wadanda ake kira ethical hackers ma'ana gwanaye ta bangaren tsaro,domin wannan nau'i sune wadanda ake samunsu a ma'aikatun gwamnati,ko manyan companies, ko bankuna, da duk manyan guraren da suke bukatar tsaro, aikinsu shine yin bincike domin gano yadda za'a inganta tsaro,
**Black hat hackers| su kuma black hat, sune yan ta'add, su kullum tunaninsu yadda za'a wargatsa tsaro, sune wadanda suke satar humimman bayanai,kudi,kayan gwamnati,satar zati da sai sauransu, a takaice su black hat su zamu iya kira barayi ko yan ta'adda, ba duka hackers ne barayi ba.
** Gray hat hackers| wannan wani gungune da sun shabam-bam da wadancan, su kuma yan tsaka tsakiyane domin lokaci daya zasu iya karya doka ma'ana suyi irin halin black hat, wani lokaci kuma suyi aiki me kyau, irin halin white hat, kunga kenan basu da wata alkibla guda daya, zasu iya samar da tsaro kuma zasu iya lalata tsaro.
Kunga kenan ba duka hackers ne barayi ko yan ta'adda ba ya danganta da manufar su
TAYAYA ZAKAYI ROOTING NA WAYARKA MENENE AMFANIN ROOTING read more
TAYAYA ZANZAMA HACKERS
Amatsayinka na dan koyo akwai hanyoyi masu yawa dazaka bi domin zama hackers, matakin farkodai shine kana bukatar ilimai daban daban,da dabaru daban daban, ka kasnce koda yaushe cikin koyo, ga wasu mahimman abubuwa da kake bukata
OPERATING SYSTEM
Idan akce Operating system mafi yawan mutane abin da suke dauka shine WINDOWS Amma a matsayinka na hacker kana bukatar, Unix based operating system ga misalinsu
Kali linuxparrot OSsunanan da yawa amma wadannan sunfi shahara
2. KA KOYI NETWORKING
MENENE NETWORKING YADDA ZAKA IYA NETWORKING DALLA-DALLA read more
Networking babban bangarene, zama kwararre a bangaren ba abune mai saukiba, sai dai zaka iya koya mataki bayan mataki kana training har ka kware,
Networking ya hada da irinsu, IP PROTOCOLS,PROXIES, VPN,TOR da sauransu
KARANTA LITTAFAI DA DARUSA A INTERNET
Amatakin koyo dole kana bukatar karanta littafai da aka rubuta akan hacking, sannan kake bibiyar darusa da ake shiryawa a internet domin yan koyo, da bibiyar website, da dai sauransu
Na Barku lafiya sai mun hadu a darasi na gaba, domin tambaya ko Neman Karin bayani, sai kuyi comment
domin kulla kasuwanci zaku iya tuntubar mu ta WhatsApp ko kira ta wannan lam
Comments
Post a Comment